Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-16 16:04:56    
Rikici bai zo karshe ba bayan yakin Iraki

cri

Jiya wato ran 15 ta wata, bangaren 'yan sanda na jihar Neineva da ke arewacin kasar Iraki ya bayyana cewa, an kai jerin hare-haren boma boman kunar bakin wake da aka dasa cikin mota har sau hudu a wasu matsugunan masu bin addinin Yazidi da ke jihar a ran 14 ga wata, inda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 250 a yayin da mutane fiye da 300 suka jikata. Wadannan su ne hare-hare mafi muni tun bayan barkewar yakin Iraki a shekara ta 2003. Haka kuma wannan ya shaida cewa, rikici bai zo karshe ba bayan yakin Iraki.

Wannan lamari ya kara daure kan gwamnatocin kasashen Amurka da Iraki da kuma kasashen duniya bisa ga irin dimbin jama'ar da suka rasa rayukansu a wadannan hare hare. Ofishin shugaban kasar Iraki Jalal Talabani ya bayar da sanarwa a ran 15 ga wata, inda ya yi kira ga 'yan kasar Iraki da su hada kansu domin yaki da makarkashiyar kawo baraka ga kasar. Kuma a ran nan, gwamnatin kasar Iraki ta sanar da cewa, domin samun kwanciyar hankali a shiyyar, gwamnatin ta tsai da kudurin aiwatar da dokar hana fitar dare a arewa maso yammacin kasar tun ranar. Haka kuma babban kwamanda na sojojin kasar Amurka da ke Iraki David Petreus da kuma jakadan Amurka da ke kasar Ryan Ceocker sun bayar da sanarwar hadin gwiwa, inda suka yi suka kan wannan hare-haren da aka kai kan fararen hula na Iraki. Bugu da kari kuma kakakin sojojin kasar Amurka Chrisopher Garver ya bayyana cewa, ko da yake ya zuwa yanzu ba a iya tabbatar da wadanda suka kai wadannan hare-hare ba, amma bisa la'akari kan dabarun da suka yi amfani da su wajen kai hare-hare, ana iya danganta su da rashen kungiyar al-Qaida da ke Iraki.


1 2 3