Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-16 16:04:56    
Rikici bai zo karshe ba bayan yakin Iraki

cri

Kasashen duniya su ma sun mayar da martani kan wannan batu. A ran 15 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya bayar da sanarwa, inda ya la'anci wannan al'amarin jefa boma-bomai a jere da kakausan harshe. Kuma ya nuna cewa, babu ko wani dalilin da zai iya zama hujjar kashe fararen hula. Ban da wannan kuma a ran nan da dare, kasar Portugal da ke jan karagar shugabancin kungiyar tarayyar Turai a wannan zagaye ta ba da sanarwar cewa, nufin hare-haren shi ne tsananta rikicin da ke tsakanin rukunonin addinai daban daban na Iraki, shi ya sa kungiyar tarayyar Turai ta yi kira ga rukunoni daban daban na Iraki da su bi hanyar zaman lafiya da samun bunkasuwa, da kuma yin watsi da dukkan al'amuran tashe-tashen hankali.

Masharhanta suna ganin cewa, dalilin da ya sa ake samun munanan hare-hare a kasar Iraki shi ne sabo da yakin Iraki da kasar Amurka ta tada ba tare da samun amincewar MDD ba.

Da farko, yakin Iraki ya karya tsarin siyasa da na moriya na lokacin da Saddam Hussein ke kan karagar mulkin kasar Iraki, kuma ya kara tsananta rikicin da ke tsakanin rukunonin addinai da kabilu daban daban. Bayan da aka kawar da mulkin Saddam, rukunin Shiite da Kurdawa sun maye gurbin rukunin Sunnite wanda ya taba shugabantar mulkin kasar Iraki. Sauyawar mulkin kasar Iraki ta haddasa sabbin rikice-rikicen da ke tsakanin rukunonin addinai da kuma kabilu daban daban na kasar, sabo da haka an ba da taimako ga al'amuran tashe-tashen hankali da laiffuffuka iri daban daba bisa wani mataki, da kuma lallata halin tsaron kai da kasar ke ciki.


1 2 3