Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-15 15:40:27    
Gasar tseren kwale-kwale ta wasan Olympics ta kawo wa Qingdao karfi

cri

A yayin da Qingdao take raya kanta zuwa birnin kwale-kwale, gine-ginen jama'a na sami babbar kyautatuwa. A shekarun baya da suka wuce, Qingdao ta soma shimfida hanya a karkashin teku da gadar ketare teku daya bayan daya, ban da wannan kuma, ta fara yin kwaskwarima kan tashar jirgin kasa ta birnin, ta yi ta fadada filin jirgin sama nata, ta kuma kafa kwarya-kwaryar tsarin zirga-zirga da ke bai wa mutane sauki. Dadin dadawa kuma, ta kaddamar da gina gine-ginen al'umma da ke da nasaba da al'adu da yawa don kara kyautata kanta a fannin harkokin al'adu.

Dangane da canje-canjen da Qingdao ta samu, 'yan wasan da ke shiga gasar tseren kwale-kwale ta 'Good Luck Beijing' ta shekarar 2007 a Qingdao, wadanda suka zo daga kasashe da yankunan daban daban na duniya, sun nuna babban yabo a wannan fanni. Malam Kellen Christophe, malamin horaswa na kungiyar kasar Mexico, ya taba zuwa Qingdao domin yin gasa, ya gaya mana cewa,'Qingdao ta sami sauye-sauye da yawa, tana yin ayyuka kamar yadda ya kamata. Ta kara raya birnin na zamani, haka kuma, 'yan birnin suna kishin bakunci. Dukkansu na da kyau kwarai.(Tasallah)


1 2 3