Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-15 15:40:27    
Gasar tseren kwale-kwale ta wasan Olympics ta kawo wa Qingdao karfi

cri

A yayin da Qingdao take share fage kan gasannin tseren kwale-kwale da kananan kwale-kwale na taron wasannin Olympic na shekara ta 2008, ta dauki matakai da yawa, wadanda 'yan birnin masu dimbin yawa suka ci gajiyarsu kwarai. Saboda haka, a ran 8 ga wata, wato rana ce da ta rage sauran shekara guda da bude taron wasannin Olympic na Beijing, dimbin 'yan birnin Qingdao sun taru a babban filin Wusi da ke tsakiyar birnin bisa son ransu, sun taya murnar wannan muhimmiyar rana.

Yanzu shekaru 6 sun wuce da Beijing ta sami damar shirya taron wasannin Olympic na shekarar 2008, kuma Qingdao ta sami zarafin taimake ta wajen shirya gasannin tseren kwale-kwale da kananan kwale-kwale. A cikin wadannan shekaru 6, shirya irin wadannan muhimman gasanni ya kawo wa Qingdao manyan sauye-sauye ba zo ba gani. Irin wadannan gasanni da kuma kwale-kwale sun zama alamu ne na Qingdao, wadanda suka bambance ta da sauran biranen kasar Sin dake bakin teku, sa'an nan kuma, Qingdao ya kasance tamkar birnin kwale-kwale. Magajin Qingdao malam Xia Geng ya gaya wa wakilinmu cewa,''Yan birnin Qingdao sun yi shekaru 6 suna namijin kokari wajen shirya gasannin tseren kwale-kwale da kananan kwale-kwale na taron wasannin Olympic na shekarar 2008 na matsayin koli kuma mai sigar musamman. Za mu ci gaba da kyautata wadannan ayyukan shirye-shirye a cikin shekara ta karshe.'

Bisa adadin da hukumar harkokin kididdiga ta Qingdao ta bayar, an ce, gasannin tseren kwale-kwale da kananan kwale-kwale na taron wasannin Olympic na shekarar 2008 sun sa kaimi kan bunkasuwar tattalin arzikin Qingdao sosai. Tun daga shekarar 2003 har zuwa yanzu, matsakaicin karuwar tattalin arzikin Qingdao na ko wace shekara ya kai kashi 16.4 cikin kashi dari, haka kuma, jimlar GDP da jimlar kudaden da ta samu dukkansu sun ninka sau daya. Irin wadannan adadin da Qingdao ta ji alfahari kansu sun kasance tamkar martani ne da Qingdao ta samu daga wajen raya kanta zuwa birnin kwale-kwale.


1 2 3