Birnin Qingdao, muhimmin birni ne da ke ba da taimako ga birnin Beijing wajen shirya taron wasannin Olympic na shekara ta 2008. A shekara mai zuwa za a shirya gasannin tseren kwale-kwale da kananan kwale-kwale na taron wasannin Olympic na Beijing a wannan kyakkyawan birni da ke gabashin kasar Sin, yana kuma bakin teku. Shirya irin wadannan muhimman gasanni yana kawo wa Qingdao sabbin ci gaba.
A ran 8 ga wata da sassafe, wani dan birnin Qingdao mai suna Zhang Ling ya je wurin shan iska da ke kusa da gidansa domin motsa jiki. Ruwa mai tsabta a cikin kogi da kuma kwarran bishiyoyi da ke gabar kogin da kyawawan furanni da kwarran ciyayi dukkansu sun faranta wa wannan tsoho mai shekaru 63 da haihuwa rai sosai. Amma duk da haka, yau da shekaru 3 da suka wuce, kogin da ke cikin wannan wurin shan iska cike yake da masu dauda, yana da wari sosai, wurin shan iskan nan kuma na lalacewa. Game da sauye-sauyen da shirya gasannin tseren kwale-kwale da kananan kwale-kwale na taron wasannin Olympic na Beijing ke kawo wa birninsa, malam Zhang ya yi zumudi kwarai, ya ce,'Mun ji matukar farin ciki saboda shirya gasannin taron wasannin Olympic a birninmu, a kofar gidana. A can da muhallin wajen bai yi kyau ba, akwai wani masana'antar kera jiragen ruwa a nan, amma saboda za a shirya gasannin taron wasannin Olympic, shi ya sa an kau da shi. Yanzu muhalli na da kyau kwarai a nan, haka kuma ruwan na da tsabta sosai.'
1 2 3
|