Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-15 15:18:51    
Kabilun kasar Sin

cri

Masu karatu, Sin kasa ce da ke da mabiyan addinai iri daban daban, kuma yawancin kananan kabilun kasar Sin suna da addinin da suke biyayya. Misali, kabilu 10 ne suke bin musulunci a nan kasar, wadanda suka hada da Hui da Uygur da Kazak da Dongxiang da Bao'an da Sala da Khalkhas da Tartar da Uzbek da Tadzhik. Akwai kuma kabilun da suke bin addinin Buddah da Krista da dai sauran addinai daban daban. Gwamnatin kasar Sin tana bayar da 'yancin bin addinin da suke ga dama ga dukan al'ummar kasar, kuma tana nuna girmamawa ga 'yancin kabilu daban daban na bin addinin da suka ga dama, kuma tana kiyaye harkokin addini da kabilu daban daban suke gudanarwa yadda ya kamata.

Ban da wannan, yawancin kananan kabilun kasar Sin suna da harsunansu na kansu, kuma dokokin kasar Sin suna tabbatar da 'yancin kananan kabilu na yin amfani da harshensu da kuma bunkasa shi. Gwamnatin kasar Sin ta kuma kafa sassan nazarin harsunan kananan kabilu, don horar da masana kan harsunan kabilu daban daban da kuma sa kaimi ga bunkasuwar harsunan kananan kabilu.

masu sauraro, mun dai yi muku takaitaccen bayani a kan kabilun kasar Sin, domin amsa tambayoyin da malama Habiba Isyaku ta ba mu. Da malama Habiba Isyaku da dai sauran masu sauraronmu, idan kuna sha'awar harkokin kabilun kasar Sin, muna kuma muku marhabin da sauraron shirinmu na "kananan kabilun kasar Sin" da Sanusi ke kawo muku a ko wace ranar Litinin, inda mu kan kawo muku labarai filla filla dangane da al'adun kabilu daban daban na kasar Sin da addinansu da yadda suke zaman rayuwarsu duka, tare da fatan shirin ba zai wuce ku ba.(Lubabatu)


1 2 3