Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-15 15:18:51    
Kabilun kasar Sin

cri

A nan kasar Sin, sakamakon cudanyar juna da kuma mu'amala da juna da kabilu daban daban suka dade suna yi, kabilun suna zaman cude-ni-in-cude-ka, wato a wuraren da 'yan kabilar Han suka fi zama, ana iya samun 'yan kananan kabilu, a wuraren da aka fi samun 'yan kananan kabilu kuma, akwai 'yan kabilar Han. Ko da yake kananan kabilun kasar Sin ba su da dimbin jama'a, amma suna barbaje kusan ko ina a makamakan filaye na kasar Sin, musamman ma a Mongoliya ta gida da Xinjiang da Ningxia da Guangxi da Tibet da Yunnan da Guizhou da Qinghai da Sichuan da dai sauran larduna da jihohi na kasar. Daga cikinsu kuma, lardin Yunnan ya kasance lardin da ya fi yawan kabilu a kasar Sin, kuma yawan kabilun da ke zama a wurin ya kai har 25.

Game da tambayar nan ta yaya gwamnatin kasar Sin take kula da kabilunta daban daban, to, amsa ita ce, a nan kasar Sin, kabilu daban daban, duk da yawan mutanensu da cigaban tattalin arzikinsu da kuma al'adunsu da addinansu daban daban, daidai suke a nan kasar Sin. Suna da hakkoki iri daya a fannoni daban daban. Tsarin mulkin kasar Sin ya tanadi cewa, "kabilu daban daban daidai suke a jamhuriyar jama'ar Sin, kuma gwamnati tana tabbatar da hakkokin kananan kabilu, tana kiyaye da kuma bunkasa zaman daidaici da hadin kai da kuma taimakon juna a tsakanin kabilu daban daban, sa'an nan tana hana nuna bambanci ga ko wace kabila ko kuma yi mata danniya."

Tsarin cin gashin kai a yankunan da kananan kabilu ke zama wata babbar manufa ce da gwamnatin kasar Sin ta dauka bisa hakikanin halin da take ciki, haka kuma wani muhimmin tsarin siyasa ne na kasar. Tsarin cin gashin kansu shi ne a karkashin jagorancin gwamnatin tsakiyar kasar Sin, kafa hukumomi masu zaman kansu a yankunan kananan kabilu, ta yadda kananan kabilu su ne suke tafiyar da harkokin kansu. A watan Mayu na shekarar 1947, Sin ta kafa yanki mai cin gashin kansa na Mongoliya ta gida, wanda ya kasance irinsa na farko a kasar. Daga baya, bi da bi ne sai aka kafa yankuna masu cin gashin kansu na 'yan kabilar Uygur da na 'yan kabilar Zhuang da 'yan kabilar Hui da kuma 'yan kabilar Tibet. Ya yanzu dai, daga cikin kananan kabilun kasar Sin 55, akwai 44 da suka kafa yankuna masu cin gashin kansu, kuma fadin yankuna masu cin gashin kansu ya dau kimanin kashi 64% na fadin kasar Sin baki daya.

Masu sauraro, kamar yadda kuka sani, Sin tana aiwatar da shirin kayyade haihuwa. Bayan kafuwar jamhuriyar jama'ar Sin, don neman kyautata ingancin al'ummar kananan kabilu da kuma gaggauta bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma a yankuna masu cin gashin kansu na kananan kabilu, Sin tana kuma aiwatar da shirin kayyade haihuwa a yankuna masu cin gashin kansu na kananan kabilu, Amma duk da haka, ta nuna sassauci ga kananan kabilunta, ta yadda saurin karuwar yawan kananan kabilu ya wuce matsakaicin saurin karuwar al'ummar kasar Sin baki daya.


1 2 3