Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-15 15:18:51    
Kabilun kasar Sin

cri

Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun malama Habiba Isyaku, wadda ta fito daga birnin Yola da ke jihar Adamawa, tarayyar Nijeriya. Malama Habiba Isyaku ta turo mana wata wasika a kwanan baya, inda ta ce, na san kasar Sin kasa ce da ke da dimbin kabilu daban daban, a gaskiya ina da sha'awa a kan harkokin kabilun kasar Sin, kuma ina da wasu tambayoyin da nake so ku amsa mana a filinku na amsoshin wasikunku, shin yawan kabilun da ke zamansu a kasar Sin ya kai nawa, kuma ko suna bin wani addini ne? Bayan haka, yaya gwamnatin kasar Sin take kula da kabilunta masu yawa?

To, gaskiyarki, malama Habiba Isyaku, tun zamanin da, Sin kasa ce da ke da kabilu masu yawa, kuma yawan kabilun da ke zaman rayuwa a nan kasar ya kai 56. Ban da kabilar Han, sauran kabilu ana kiransu kananan kabilu sabo da yawan mutanensu ba shi da yawa idan an kwatanta shi da na kabilar Han. To, domin amsa tambayar malama Habiba Isyaku, bari mu dan yi bayani a kan kabilun kasar Sin.


1 2 3