Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-15 15:17:18    
An kiyaye al'adun gargajiyar Tibet yadda ya kamata

cri

Direktan ofishin kula da harkokin fadar Budala Mr Qiangbagesan da ke da shekaru 65 da haihuwa shi ne mashahurin kwararren kiyaye kayayyakin tarihi, ya yi aikin cikin shekaru fiye da 20. Ya ce, kowane dakin fadar Budala na da labarinsa, kuma kowane zanen da ke kan jikin bangon fadar na da tarihinsa, kiyaye su da kyau aiki ne mai muhimmanci sasai ga gwamnatin kasar Sin da kwararru, daga shekaru 80 na karnin da ya shige, gwamnatin tsakiya ta riga ta ware kudade da yawansu ya kai kudin Sin Yuan miliyan 200 don gyara fadar, yanzu karo na biyu ne da ake gyara ta. Malam Qiangbagesan ya bayyana cewa, a wannan karon, ba a gyara babban dakin fadar nan kawai ba, wato za a mai da hankali ga gyara tushen fadar da jikunan bangwaye sosai, duk domin fadar na da tsayi sosai, in tushenta ya sami cikas wajen inganci, to abu maras kyau ne ga ingancin fadar , saboda haka, aikin gyara ya zama aiki mai muhimmanci gare mu, kuma za mu mai da hankali ga gyara rufinta da jikin bangunanta.

Domin kawar da cikas da aka samu bisa sakamakon samun masu yawon shakatawa da yawa, shi ya sa daga ranar 1 ga watan Mayu na shekarar 2003, an soma kayyade adadin masu yawon shakatawa.


1 2 3