
A jihar Tibet da ke kudu maso yammacin kasar Sin, ba ma kawai da akwai duwatsu masu rufewar kankara mai taushi da tabki mai tsarki da sauran ni'imtattun wuraren halittu ba, hatta ma da akwai shahararrun al'adu iri iri da yawa tare da fadar Budala mai girma da haikalin ibada na Dazhao da sauran wurare masu ni'ima sosai da ke dacewa da al'adun 'yan Adam, har da wakokin tarihi da aka yada su a baka dangane da jarumai da wasannin Tibet. Yau za mu gabatar da wasu abubuwa dangane da birnin Lasa, hedkwatar jihar Tibet da kuma dudduba yadda aka kiyaye al'adun Tibet.
Tsohon sarkin Tibet mai suna Sonzanganbu shi ne ya gina fadar Budala a karni na 7 don yin bikin auren gimbiya ta kabilar Han ta daular Tang mai suna Wencheng, sa'anan kuma, sarakunan Dalai na zuri'u daban daban sun yi zama a fadar. A cikin shekaru fiye da dubu, ba ma kawai fadar Budala ta zama tsarkakken wurin yada addinin Buddah ba , hatta ma ta zama alamar al'adun Tibet mai muhimmanci sosai bisa sakamakon fasahohinta da darajar tarihinta tare da kayayyakin tarihi masu yawan gaske da take tanadinsu.
1 2 3
|