Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-13 15:24:17    
Taron baje koli na goma na kimiyya da fasaha na birnin Beijing

cri

Ban da wannan kunma Madam Chen ta bayyana cewa, shirye-shiryen kwamfuta na wannan mutum-mutumin na'ura yana da sauki. Kullum ana bukatar mintoci 7 ko 8 wajen dafa naman dabbobi, kuma ana bukatar mintoci 3 kawai wajen dafa kayayyakin lambu, haka kuma dafa abinci ba zai samar da hayakin mai ba, shi ya sa yakr iya kiyaye muhallin halittu sosai.

Bayan da Zheng Hong, wani mazaunin birnin Beijing ya ga wannan mutum-mutumin na'ura, ya yi yabo sosai, kuma ya gaya mana cewa, wannan abu mafi ban mamaki ne da ya taba gani.

"Ban taba ganin irinsa a da ba. Wannan mutum-mutumin na'ura yana da ban sha'awa da ban mamaki da kuma na zamani. Kuma ya shaida cewa, ana iya fitar da mutane daga ayyukan gida. Yanzu kimiyya da fasaha ya samu bunkasuwa sosai, shi ya sa ba za a bukaci mutane wajen yin wasu ayyukan gida ba. Musamman ma game da matasa da suke shan aiki sosai. Muddin su ajiye kayayyakin lambu a cikin kwano da safe, sai za su iya cin abinci kai tsaye bayan da suka koma gida da tsakar rana."

Akwai dakunan nune-nune 10 na wannan taron baje koli na kimiyya fasaha, kuma kayayyakin nune-nune sun hada da fasahohi da kayayyakin da ke da nasaba da wasannin Olympics na shekara ta 2008, da kayayyakin kimiyya da fasaha na tattalin arziki da ake rayawa ta hanyar kimiyya da dai sauransu. Ban da wannan kuma wannan taron baje koli ya tattara kayayyakin kimiyya da fasaha da ke da nasaba da zaman yau da kullum na mutane sosai, shi ya sa sun jawo hankulan mutane sosai.

Mr. Cheng Peng ya zo daga lardin Jiangsu da ke gabashin kasar Sin, kuma wannan shi ne karo na farko da ya shiga taron baje koli na kimiyya da fasaha. Kuma ya gaya wa wakilinmu cewa,

"na riga na ziyarci dakunan nune-nune uku, kuma kayayyakin da ke da nasaba da zaman rayuwar fararen hula sun burge ni sosai. Kuma na nuna sha'awa sosai kan irin wadannan kayayyaki. Bayan da na gan su, na yi la'akarin cewa, mai yiyuwa ne zan iya yin amfani da su nan gaba."


1 2 3