Mutum-mutumin na'ura da ke iya dafa abinci, da masai da ake iya tsabtace shi da ruwa kadan, da kuma allon zane-zane na zamani da ake iya shigad da zane-zane da aka yi a kan shi cikin na'urar kwamfuta kai tsaye, wakilinmu ya ga duk wadannan abubuwa masu ban sha'awa ne a gun taron baje koli na goma na kimiyya da fasaha da aka yi a birnin Beijing ba da jimawa ba. To, a cikin shirinmu na yau, za mu je wannan taron baje koli domin ganin irin wadannan kayayyakin kimiyya da fasaha na zamani masu ban sha'awa.
A gun taron, mutum-mutumin na'ura da ke iya dafa abinci ya jawo hankulan masu kallo sosai. Madam Chen Fang, mai ba da lacca kan wannan mutum-mutumin na'ura ta bayyana cewa, bayan da aka ajiye kayayyakin lambu a cikin kwano, wannan mutum-mutumin na'ura zai iya dafa abinci da kansa. Dalilin da ya sa haka shi ne sabo da na'ura mai kwakwalwa da aka sanya a cikin mutum-mutumin na'ura tana iya kara zafin dafa abinci bisa zafin da aka tsara bisa halin musamman na kayan lambu, da kara miya a ciki, da kuma motsa abin da ake soyawa. Idan ana son dafa abinci bisa bukatunsa, to yna iya canja hanyar kara zafi da ire-iren miya da kuma yawanta. Yanzu irin wannan mutum-mutumin na'ura yana iya dafa daruruwan ire-iren abinci. Kuma Madam Chen ta kara da cewa,
"Mun ajiye girke-girke a cikin na'urar kwamfuta, kana iya zabr daya daga cikinsu bisa bukatunka. Lokacin da ake bukatar kara miya da kuma bininga a cikin abinci, mutum-mutumin na'ura zai yi da kansa. Muddin ka ajiye kayayyakin lambu a cikin kwano, da kuma zabar shirin da ake so na kwamfuta, shi ke nan, mutum-mutumin na'ura zai fara dafa abinci."
1 2 3
|