Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-13 10:53:56    
Kalubale ga kasar Somaliya dake neman samun sulhuntarwa a duk kasa

cri
 

Bisa wannan halin da ake ciki,ko da ya ke kungiyar kotunan Islama da sauran kungiyoyi masu adawa sun bayyana cewa suna adawa da kiran taron sulhuntarwar kasa,gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya ta kuduri aniyar kiran taron cikin lokaci.A gabannin kiran taron madugun dakarun dake karkashin kungiyar kotunan Islama ya yi kurarin cewa dakarunsa za su kara kai farmaki mai zafi lokacin da ake taron,haka kuma za su yanke "hukuncin kisa" ga dukkan mahalartan taron. A gabanin lokacin kiran taron,manazartan al'amuran duniya sun yi nuni da cewa kira taron sulhuntarwa zai kara dagula al'amuran kasar Simaliya dake kara tabarbarewa yayin da kungiyar kotunan Islama ta kin yarda da tattaunawa da gwamnatin wucin gadi.

A sa'I daya ko taron sulhuntarwa zai samu ra'ayi daya,da wuya a tabbatar da shi saboda kungiyar kotunan Islama musulmi ba ta halarci taron sulhuntawar ba. A halin yanzu da akwai 'yan tsohuwar majalisar dokoki ta wucin gadi da shugaban majalisar da shugaban kungiyar kotunan Islama masu adawa da gwamnati wajen talatin suna zaman hijira a ketare.Kwanan baya sun sanar da cewa za su kira wani taron sulhuntar kasa daban a watan Satumba a wani wuri dake waje da kasar Somaliya.Manazartan suna masu ra'ayin cewa idan taron sulhuntrwar al'umma da ake yi a yanzu ba zai iya samar da wani yanayin yin tattaunawa ba,to da wuya a samu sulhuntarwa tsakanin kungiyoyin Somaliya da suke yake yake cikin dogon lokaci. Jama'a masu sauraro,wannan ya kawo karshen shirinmu na duniya ina labari.mun gode muku sabo da kuka saurarenmu.(Ali)


1 2 3