A cikin shirinmu na yau,za mu kawo muku wani bayanin da wakilin kamfanin dillancin labarai na Hsinhua ya rubuta a kan cewa kalubale ga kasar Somaliya dake neman samun sulhuntarwa a duk kasa. Tun lokacin da aka bude taron sasantawa ta duk kasa ta kasar Somaliya a babban birnin Mogadishu a tsakiyar watan Yuli, al'amuran kasar Somaliya ba su samu kyautatuwa ba.
Tashe tashen hankula da hare hare dake kara tsamari sun bayyana cewa kasar Somaliya tana fuskantar kalubale wajen neman samun sulhuntarwar al'umma bayan aka kira taron sasautarwa. Tun bayan da aka kira taron sulhuntarwa,hare haren da aka kai a wuraren daban daban na kasar Somaliya ya yi ta karuwa.
Tun daga daren ran daya zuwa ran biyu ga watan nan,an samu arangamar dakaru da hare hare da dama a birnin Mogadishu,a kalla dai sun haddasa mutuwar mutane goma kuma kimanin mutane 29 ne suka jikkata.Tun daga daren ran 10 zuwa ran 11 ga wata,an kashe wakilai guda hudu da suka halarci taron sulhuntarwar kasa da jami'ai biyu na gidan rediyo mai zaman kansa,wadanan mutane da aka kashe sun zama mutane ne da suka rasa rayukansu a cikin sabon zagaye na hare hare a wannan kasar dake kuriyar Afrika.
1 2 3
|