Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-13 10:53:56    
Kalubale ga kasar Somaliya dake neman samun sulhuntarwa a duk kasa

cri
 

Tun farkon farko an yi shirin kiran taron sulhuntarwar al'ummar kasar Somaliya a tsakiyar watan Afril na bana duk domin kawar da kiyayya tsakanin kungiyoyin daban daban da samar da zaman lafiya.An jinkirtar da taron zuwa tsakiyar watan Yuni sabo da yake yake na hauhawa a watan Maris da watan Afril na bana a Mogadishu,daga baya an sake jinkirtar da lokacin taron zuwa ran 15 ga watan Yuli sabo da ayyukan ba da guzuri da shirin ba su kai yadda ya kamata ba.Ko ma a gabannin kira taron wasu mutane suna shakkun kiran taron cikin lokaci.

Daga bisani,shugaban kasar Somaliya Yusuf ya bayyana cewa " ya kamata a kira taron sulhuntarwa na duk kasa bisa shirin da aka tsara ko ma Mogadishu ya sha hari da makaman nukiliya ne." Gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya tana da dalilai da dama domin kira taron sulhuntarwar kasa.a gefe daya,kasashen duniya suna masu ra'ayin cewa makomar zaman lafiyar Somaliya ta danganta da sulhuntarwa ba da dakaru ba.Amurka da kungiyar tarayyar Turai sun matsa lamba ga gwamnatin wucin gadi ta Somaliya da ta yi tattaunawa da kungiyoyi masu adawa da gwamnati.a wani gefe daban,Habasha ta tura sojoji ta taimakawa gwamnatin wucin gadi ta Somaliya wajen murkushe dakarun dake karkashin kungiyar kotun Islama wadda ita ce muhimmiyar abokiyar gaba ta gwamnatin wucin gadin,A cikin rabin shekara da 'yan kai na bana da ya shige,Habasha na fuskantar matsin janye sojojinta daga Somaliya..Amma watanni kalilan ne da aka kafa rundunar sojan tsaron kasar Somaliya,gwamnatin wucin gadi ta Somaliya ba ta da karfin tinkarar dakaru masu adawa da gwamnati cikin yanci ba,sai ta mika rokon tura sojoji ga kungiyar tarayyar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya.Kwamitin sulhu na MDD ya ba da shawara cewa kamata ya yi gwamnatin wucin gadi ta Somaliya ta yi shawarwari da kungiyoyi masu adawa da farko da kago wani yanayin kwanciyar hankali,sa'an MDD ta yi la'akarin tura sojoji.


1 2 3