Idan ba a dauki tsauraran matakan yaki da kasuwanni na bayan fage ba, to labuddah akwai kamfanoni da masana'antu masu yawan gaske da za su shiga cikin wadannan kasuwanni na bayan fage duk domin samun moriya. Yin haka zai dakushe aniyar kamfanoni da masana'antu ta bada taimakon kudi ga gudanar da taron wasannin Olympic, kuma za a kasa samun taimakon kudi wajen bunkasa harkar wasannin Olympic; har gwamnatin birnin Beijing ba za ta iya gudanar da gagarumin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 ba.
A karshe dai, Mr. Chen Fong ya jaddada, cewa yaki da kasuwannin bayan fage, bukatu ne na kiyaye moriyar kamfanoni da masana'antu masu bada taimako ga wasannin Olympic, kuma ya kasance tamkar alkawari ne da muka dauka ga kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa; haka kuma ya zama tamkar daya cikin muhimman alamomi na gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008 cikin nasara.( Sani Wang ) 1 2 3
|