|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2007-08-03 15:27:54
|
|
Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing na kokarin kiyaye moriyar kamfanoni masu ba da taimako ga gudanar da taron wasannin
cri
Ma'anar kasuwannin bayan fage ita ce, wani irin aikace-aikace ne na yin cudanya ta kariya tare da taron wasannin Olympic don cin riba da wadancan kamfanoni da masana'antu wadanda ba su bada taimako ba sukan yi ba tare da samun izini ba. Alal misali: wasu 'yan kasuwa masu samun izinin musamman na tafiyar da harkokinsu da ba na taron wasannin Olympic ba sun yi sarrafe-sarrafe ko sayar da hajjojin dake da lambobin taron wasannin Olympic; Ban da wannan kuma, wasu kamfanoni da masana'antun da ba su bada taimako ga gudanar da taron wasannin Olympic ba sun yi amfani da kalmomin " taron wasannin Olympic" da " Beijing 2008" da dai sauransu lokacin da suke yin talla ko farfagandar kasuwanci. Hakan ya sa jama'a suka yi tsammanin cewa wadannan kamfanoni da masana'antu suna da alaka tsakaninsu da taron wasannin Olympic. Mr. Chen Fong ya kara da cewa: " Lallai wadannan 'yan kasuwa ko kamfanoni da masana'antu sun saba wa ka'idar yin takara bisa adalci. Aikace-aikacen da suka yi sun yi babbar illa ga yunkurin raya kasuwannin Olympic ,da tauye iko da moriya na kamfanoni da masana'antun da suka bada taimako ga gudanar da taron wasannin Olympic da kuma rage daraja irin ta kasuwanci ta lambobin Olympic".
1 2 3
|
|
|