Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-03 15:27:54    
Kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing na kokarin kiyaye moriyar kamfanoni masu ba da taimako ga gudanar da taron wasannin

cri

Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, gudanar da wani gagarumin taron wasannin Olympic cikin nasara ba ya rabuwa da kwarewar 'yan wasa , da cikakkun shirye-shirye na masu shirya taron wasannin da kuma alla-allar shiga cikin harkokin wasannin da 'yan kallo sukan yi; Haka kuma ba da tabbaci ga samar da isassun kudade, wani sharadi ne da ya wajaba na gudanar da taron wasannin Olympic cikin nasara. Wasu kudade masu tarin yawa da ake bukata wajen gudanar da taron wasannin Olympic, a kan samo su ne daga hannun 'yan kasuwa masu bada taimako ga gudanar da taron wasannin. Wadannan 'yan kasuwa dai suna kishin samun tabbaci wajen cin moriyarsu lokacin da suke bada taimakon kudi. A duk tsawon lokacin da ake share fage ga gudanar da taron wasannin Olympic na Beijing, kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing na sanya kokari matuka ta hanyoyi da dama wajen kiyaye iko da moriya na halal na kamfanoni da masana'antu masu bada taimako.

Bunkasuwar harkar wasannin Olympic da gudanarwar taron wasannin Olympic cikin nasara, dukansu suna bukatar samun taimakon isassun kudade. Akasarin kudaden da aka samu wajen gudanar da taron wasannin Olympic na Bejing, an samo su ne daga yunkurin raya kasuwanni. Saboda haka, abin ya zama mafi muhimmanci ga kiyaye iko da moriya na 'yan kasuwa masu bada taimako ,da 'yan kasuwa masu kula da harkokin watsa shirye-shiryen wasanni ta telebijin, da kuma 'yan kasuwa da aka basu iznin musamman na sayar da kayayyaki na game da taron wasannin Olympic. A " Gun taron watsa labarai kan kiyaye ikon mallakar ilimi a fannin Olympic da yaki da kasuwannin bayan fage" da aka gudanar kwanakin baya bada dadewa ba, Mr.Chen Fong, mataimakin minista mai kula da harkokin raya kasuwanni na kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing ya bayyana ayyukan da kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing yake yi na kiyaye iko da moriya na kamfanoni da masana'antu masu bada taimako, musamman ma na riga-kafin kasuwannin bayan fage.


1 2 3