
Wasu manazarta sun yi hasashen cewa, 'Kwalliya ta biya kudin sabulu' idan bangarorin biyu sun kai ga cimma daidaito kan batun kafa kasar Palasdinu sakamakon shiga tsakani da Madam Rice ta yi; Hakan ya kasance wani babban ci gaba ne da aka samu wajen gudanar da yunkurin shimfida zaman lafiya a yankin Palasldinu da Isra'ila. Kamar yadda shugaba Abbas ya fadi cewa, wannan dai a kalla zai iya barin Palasdinawa ganin siffar kasarsu ta nan gaba. Amma a lokaci daya, wasu masharhanta sun bayyana ra'ayinsu cewa, amfani kadan ne Madam Rice ta bayar ga daidaita rikicin dake tsakanin Palasdinu da Isra'ila, wanda ya ki ci ya ki cinyewa saboda bangarorin biyu ba su warware wasu muhimman sabane-sabane dake kasancewa tsakaninsu ba, wadanda kuma mai yiwuwa ne za su banzatar da duk kokarin da aka yi a da. Kazalika, manufar ci gaba da yi wa kungiyar Hamas saniyar-ware da gwamnatin Amurka ke aiwatarwa ita ma ba za ta bada taimako ga kafa kasar Palasdinu ba. Kungiyar Hamas ta ce Madam Rice ta zo nan ne ba domin taimakon kafa kasar Palasdinu ba, ai kara janyo baraka ne ga al'ummar Palasldinu. ( Sani Wang ) 1 2 3
|