Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-03 10:50:04    
Ziyarar Rice a Palasdinu da Isra'ila ta kirkiro irin muhalli ga gudanar da taron kasa da kasa kan batun Gabas ta Tsakiya

cri

An labarta cewa, sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka Madam Condoleezza Rice ta kammala ziyara ta gajeren lokaci a yankin Palasdinu da Isra'ila jiya Alhamis. Ra'ayoyin bainal jama'a sun lura da cewa, a cikin shekaru biyu da 'yan watanni da suka gabata bayan da Madam Rice ta kama mukamin sakatariyar harkokin wajen kasar Amurka, ta taba kai ziyara ba sau daya ba ba sau biyu ba a yankin Palasinu da Isra'ila. A cikin duk tsawon lokacin ziyarce-ziyarcen, sau da dama ne ta jaddada cewa wai ta zo nan yanki ne don sauraron ra'ayoyin da bangarori biyu wato Palasdinu da Isra'ila suka dauka. Amma a ziyarar da ta yi a wannan gami, Madam Rice ta sha nemansu da su yi shawarwari irin na ' zahiri' tsakaninsu. Ta yi hakan ne domin share fagen taron kasa da kasa kan batun Gabas ta Tsakiya wanda shugaba Bush na kasar Amurka ya bada shawarar kiransa.

Bisa halin da ake ciki yanzu, ana ganin cewa, nasara mafi girma da Madam Rice ta samu bisa ziyarar da ta yi a wannan gami ita ce, ta sa bangarorin biyu wato Palasdinu da Isra'ila suka cimma daidaito kan yadda za su yi shawarwarin shimfida zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya. Idan ba a manta ba, tuni shugaba Mahmoud Abbas na hukumar Palasdinu ya bayyana fatansa na yin shawarwari tare da Isra'ila a game da batun kan iyakokinsu, da matsayin karshe na Kudus da kuma ikon komawar 'yan gudun hijira na Palasdinu da dai sauran batutuwa ; Amma gwamnatin Isra'ila ta yi watsi da yin haka. Ana ganin cewa, bangarorin biyu sun yin dan rangwame a wannan gami saboda Madam Rice ta shiga tsakani wajen warware wannan magana. Yayin da Madam Rice ta gana da shugaba Abbas jiya Alhamis ta furta cewa, firaminista Ehud Olmert na Isra'ila ya rigaya ya yarda da yin tattaunawa tare da bangaren Palasdinu kan wasu ' Muhimman batutuwa'; Amma a nasa bangaren, shugaba Abbas ya amince da shirin da Mr. Olmert ya gabatar kafin wannan lokaci a kan cewa bangarorin biyu su rattaba hannu kan wata ' Sanarwar ka'ida' dake kunshe da wasu yarjejeniyoyi irin na manyan tsare-tsare game da batun kafa kasar palasdinu kafin su yi shawarwari dalla-dalla kan batun matsayin karshe na Kudus.


1 2 3