|
|
 |
 |
| Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
| (GMT+08:00)
2007-08-03 10:50:04
|
 |
|
Ziyarar Rice a Palasdinu da Isra'ila ta kirkiro irin muhalli ga gudanar da taron kasa da kasa kan batun Gabas ta Tsakiya
cri
|

Ko shakka batu rangwamen da Palasdinu da Isra'ila suka yi ya bude hanya ga yin shawarwari da dama tsakanin bangarorin biyu kafin a gudanar da taron kasa da kasa kan batun Gabas ta Tsakiya. A watan jiya, shugaba Bush na Amurka ya yi kiran gudanar da taron kasa da kasa kan batun Gabas ta Tsakiya don ingiza yunkurin shimfida zaman lafiya a wannan shiyya. Ana sa ran za a gudanar da wannan taro a watan Nuwamba na shekarar da muke ciki. Jiya a Ramallah, Madam Rice ta fadi cewa, shugaba Bush ya yi kiran gudanar da wannan taro ne domin yana fatan bangarorin biyu za su yi shawarwari irin na zahiri a kokarin kafa kasar Palasdinu tun da wuri. Bangarorin biyu sun yarda da yin shawarwari a tsanake kafin a gudanar da wannan taro tare da bayyana aniyarsu ta tabbatar da shirin manyan tsare-tsare a game da batun kafa kasar Palasdinu da kuma aza harsashi ga gudanar da wannan taro cikin nasara.
1 2 3
|
|
|