Mr Hu Jintao ya kara da cewa, wajibi ne, a mayar da darikar samun bunkasuwa ta hanyar kimiyya bisa matsayin manufa mai muhimmanci da ake bi don inganta ayyukan tsaron kasa da raya rundunar sojojin kasar, ta yadda za a mayar da ayyukan tsaron kasa da rundunar sojojin kasar da su zama iri na zamani. Ya ce, "wajibi ne, mu fahimci sabon ci gaban aikin soja a duniya da sabon bukatu da ake yi wajen raya kasarmu, mu aiwatar da manufar raya harkokin tsaron kasa da na tattalin arziki cikin daidaituwa, a sakamakon kara samun ci gaba a fannin tattalin arzikin kasa, za mu kara ware kudi masu yawa wajen inganta harkokin tsaron kasa sannu a hankali, ta yadda za mu yi ta daga matsayin zamanintar da harkokin tsaron kasa da rundunar sojojinta, mu yi kokari wajen inganta aikin tsaron kasa da rundunar sojoji wadanda ke dacewa da zaman lafiyar kasa da moriyar bunkasuwa."
A gun babban taron da aka yi a yau, an nuna yabo ga jarumai da yawa na rundunar sojojin jama'ar Sin ta kwatar 'yancin kasa. Yang Liwei, dan sama jannati na farko na kasar Sin ya bayar da jawabi a madadin jaruman cewa, "bisa matsayina na wakilin jarumai, na fahimci babban nauyi da muke sauke wa a bisa wuyanmu. Dole ne, mu yi kokari sosai wajen yadada kyakkyawar al'adar rundunar sojojinmu game da bin umurnin Jam'iyyar Kwaminis ta Sin da bauta wa jama'a da nuna jaruntaka da kwarewa ga yaki, mu ta ka muhimmiyar rawa wajen kara ba da babban taimako ga raya rundunar sojojinmu ta zamani, da ba da sabon taimako ga jam'iyyar da jama'ar kasar." (Halilu) 1 2 3
|