Da ma a farkon kafuwarta, burin kungiyar PLO shi ne murkushe akidar siyasa ta Yahudawa daga fannonin siyasa da tattalin arziki da soja da al'adu ta hanyar nuna karfin soja, sa'an nan, a kafa kasar Palasdinu a yankin Palasdinu. Kungiyar ta taba fafatawa a kasashen Jordan da Lebanon a matsayin sansanoninta. Bayan da Isra'ila ta kutsa kai cikin Lebanon a shekarar 1982, PLO ta sha asarori a fannin soja, ba yadda ta yi sai ta janye jikinta daga birnin Beirut.
Sakamakon sauye-sauyen halin da ake ciki a gabas ta tsakiya, kungiyar PLO ta fara daukar sassaucin matsayi kan batun Palasdinu. A ranar 15 ga watan Nuwamba na shekarar 1988, an zartas da sanarwar siyasa da sanarwar samun 'yancin kai a gun taron musamman na majalisar kasa ta kungiyar, inda aka sanar da amincewa da kuduri mai lambar 242 da 338 na MDD, aka kuma sanar da kafuwar kasar Palasdinu.(Lubabatu) 1 2 3
|