Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-08-01 16:53:47    
Kungiyar 'yantar da Palasdinu

cri
Tambayar da za mu amsa a wannan mako ta fito ne daga hannun Yakubu Mohammed Rigasa, mai sauraronmu da ya fito daga jihar Kaduna, tarayyar Nijeriya. A kwanan baya, malam Yakubu Mohammed Rigasa ya rubuto mana cewa, wai shin me ya faru da kungiyar nan ta Palestine Liberation Organisation, wato PLO ta marigayi malam Yasser Arafat? Tun da Arafat din ya rasu na daina jin duriyar kungiyar, sai dai kungiyoyin Fatah da Hamas kadai nake jin kuna ambata.

A hakika, kungiyar 'yantar da Palasdinu, wato Palestine Liberation Organization, ko kuma PLO a takaice, na kunshe da kungiyoyin siyasa iri daban daban guda takwas, ciki har da kungiyar neman 'yancin kan al'ummar Palasdinu, wato Fatah. Domin amsa tambayar malam Yakubu Mohammed Rigasa, a cikin shirinmu na yau, bari mu dan gutsura muku tarihin kungiyar ta PLO.

An dai kafa kungiyar PLO ne a watan Mayu na shekarar 1964 a birnin Kudus, sa'an nan, a shekarar 1968, bisa shawarwarin da PLO ta yi tare da sauran kungiyoyin Palasdinu, sun zartas da "tsarin ka'idojin jama'ar Palasdinu", inda suka tsai da cewa, kungiyar PLO ta kasance wakiliya ta kungiyoyi daban daban na Palasdinu, kuma tana daukar nauyin maido da yankunan Palasdinu da kuma komar da jama'ar Palasdinu da ke gudun hijira gida. Daga baya, a shekarar 1974, a gun taron shugabannin kasashen Larabawa na karo na bakwai da aka yi a birnin Rabat, babban birnin kasar Morroco. an tsai da kungiyar PLO a matsayin kungiya daya rak da ke da halalcin wakiltar jama'ar Palasdinu. Sai kuma a watan Nuwamba na shekarar, MDD ta gayyaci kungiyar ta PLO da ta halarci taronta a matsayin mai sa ido. Daga bisani a shekarar 1976, bi da bi ne kungiyar ta zama mamba na kungiyar 'yan-ba-ruwanmu da na kawancen kasashen Larabawa. Daga baya, kungiyar ta kuma kulla hulda iri daban daban tare da kasashe sama da 100.


1 2 3