Marigayi Yasser Arafat na kan kujerar shugabancin kwamitin tsakiya na kungiyar nan ta PLO tun daga shekarar 1970, kuma Mahmoud Abbas ya maye gurbinsa bayan da ya riga mu gidan gaskiya a watan Nuwamba na shekarar 2004.
Kungiyar PLO tana da majalisar kasa ta Palasdinu a matsayin hukumarta ta koli. A kasar Palasdinu, kungiyar PLO da hukumarta ta koli, wato majalisar kasa ta Palasdinu, suna kasancewa kafada da kafada da hukumar ikon Palasdinu da kuma hukumarta ta koli ta majalisar dokokin Palasdinu.
Daga cikin kungiyoyin siyasa takwas na kungiyar PLO, Fatah ita ce ta fi karfi da ba da tasiri da kuma yawan mutane, kuma tana rike da babban ikon kungiyar PLO a fannonin soja da siyasa da kudi da kuma harkokin waje, wato tana taka rawar jagoranci a cikin kungiyar PLO.
1 2 3
|