Tsoffafin itace da aka samu a gidan ibada na Tanzhesi abu ne daban da ke jawo hankalun mutane. Itacen Tricuspid Cudrania wato Zheshu a bakin Sinawa, itace ne mai daraja, su ne kuma dalilin da ya sa gidan ibada na Tanzhesi ya shahara. Ana amfani da ganyayensu domin kiwon tsutsotsin samar da siliki wato silkworms, sa'an nan kuma, ana amfani da rassansu domin samar da kayayyakin daki. A bayan wannan gidan ibada, akwai wani karamin tabki, wato Tan a bakin Sinawa, ban da wannan kuma, itacen Zheshu na girma sosai a babban dutse a wajen, shi ya sa ake kiran wannan gidan ibada da sunan Tanzhesi, wato gidan ibada da ke da karamin tabki da kuma itacen Zheshu. Tsoffafin itacen Zheshu da aka samu a nan na da tsayi, sun kuma samar da inuwa mai fadi, a ko ina a wajen ana iya sauraren kukan tsuntsaye. A cikin gidan ibada na Tanzhesi, ya kasance da wani icen gingko mai tsawon shekaru dubu. Tsayinsa ya wuce mita 40, mutane 7 ko 8 suna iya kewaye jikinsa hannu da hannu. A lokacin zafi, tsohon icen nan na samar da inuwa mai fadin murabba'in mita 600. A lokacin kaka kuwa, dukkan ganyayensa sun zama rawaya, sun faduwa daga icen, sai ka ce rawayan malam-bude-littafi da yawa na tafiya a sararin sama, wannan na da kyan gani ainun.
Haka zalika kuma, a gidan ibada na Tanzhesi, tsoffafin itacen magnolia 2 masu launin shuni sun zama kan gaba a cikin dukkan furanni. An ce, tsawon shekarun dukkansu ya wuce dari 4. A yayin da aka fid da furannin magnolia a lokacin bazara, wadannan itacen magnolia sun jawo dubban masu yawon shakatawa. Madam Wang Lin tana matukar kishin furen magnolia, ta ce,
'Na zo daga gundumar Chaoyang ta birnin Beijing. Yau na ji cewa, an riga an fid da furannin magnolia a nan, shi ya sa na zo wajen domin jin dadin kallonsu. Suna girma sosai, na yi farin ciki sosai bayan da na gan su.'
Gidan ibada na Tanzhesi a yau ya jawo masu yawon shakatawa daga wurare daban daban saboda wuraren gargajiya masu yawa da kuma kyan karkara, sa'an nan kuma, ya raya ayyukan zamani don ba da hidimomin yawon shakatawa. Shi wani mashahurin wurin yawon shakatawa ne a waje da birnin Beijing.(Tasallah) 1 2 3
|