Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-31 15:29:55    
Gidan ibada na Tanzhesi mai tsawon shekaru dubu a Beijing

cri

A kewayen birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin, akwai tsoffafin gidajen ibada da yawa, inda masu yawon shakatwa da ke ziyara a Beijing suke zuwa kullum. Gidan ibada na Tanzhesi mai tsawon shekaru dubu da ke yammacin Beijing na daya daga cikin irin wadannan gidajen ibada.

Gidan ibada na Tanzhesi wani tsohon gidan ibada ne da aka gina shi a gindin babban dutse, a kewayensa kuma akwai manyan duwatsu 9. An gina shi a shekarar 307 bayan haihuwar Annabi Isa A.S., wato ke nan tarihinsa ya wuce shekaru dubu 1 da dari 7, wanda ya fi na Beijing a matsayin hedkwatar kasar dadewa. Malam Hao Xinjian, mai ba da taimako ga darektan hukumar kula da gidan ibada na Tanzhesi, ya yi karin bayanin cewa,

'A shekarar 307, a arewancin kasar Sin, madam Hua Fang, matar babban kantoma mai suna Wang Jun, ta rasu. Mijinta Wang Jun ya binne ta a yankin Babaoshan da ke yammacin Beijing. Sa'an nan kuma, ya gina gidan ibada na Jiafusi domin neman kawo wa matarsa da kuma duk kasarsa alheri a yammacin Beijing a wannan shekara. Gidan ibada na Jiafusi shi ne aka samu asalin gidan ibada na Tanzhesi daga wajensa.'


1 2 3