Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-31 15:29:55    
Gidan ibada na Tanzhesi mai tsawon shekaru dubu a Beijing

cri

Bayan kafuwar gidan ibada na Tanzhesi, sarakuna na dauloli daban daban na kasar Sin suna kishin kai ziyara a wajen, saboda haka ko girman gine-ginensa, ko kuma matsayinsa a rukunin addinin Buddha na kasar Sin, wannan gidan ibada ya zama kan gaba a cikin gidajen ibada masu yawa a Beijing.

In wani ya kai ziyara a gidan ibada na Tanzhesi, bai kamata ba ya bar gidan ba tare da ya ga babbar tukunyar da aka kera da tagulla domin dafa abinci. Ita ce dukiya ga wannan gidan ibada. Diameter na tukunyar ya kai mita 4, zurfinta ya kai mita 2. A kan kashe sa'o'i fiye da 10 ana kafa kunu a cikinta. An kuma sassaka kalmomin 'Tanzhesi' a kan murhu. Malam Hao ya yi bayani kan dalilin da ya sa aka sassaka wadannan kalmomi a kan murhun, ya ce,

'Almara ta ce, tsohon limanin da ke gidan ibada na Tanzhesi ya ji tsoron gamuwa da gobara a gidan ibadan nan, saboda an gina dukkan gine-ginensa ne da katako, wanda ya kan gamu da gobara cikin sauki. Wata rana ya yi mafarki, inda aka ce, in an sa gidan ibada na Tanzhesi a kan wuta, to, zai tsira daga gobara. Bayan da ya tashi, ya yi tunani, sai ya yi dabara ba zato ba tsammani, in an sassaka sunan wannan gidan ibada wato 'Tanzhesi' a kan murhu, to, suna kan wuta a ko wace rana, ta haka, gidan ibadan ya tsira daga gobara. Shi ya sa, ya sassaka kalmomin Tanzhesi a kan murhun.'

Ban da wannan babbar tukunya, wata dukiya daban a gidan ibada na Tanzhesi ita ce kifin dutse, wanda ya shahara sosai. Tsawonsa ya kai mita 1.7, nauyinsa ya kai kilo 150, launinsa kore ne mai duhu. A idanun mazaunan wurin, wannan kifin dutse na iya shawo kan cututtuka.

A zahiri kuma, masu sana'a ne suka sassaka wannan kifin dutse daga dutsen da ya fado a kan doron kasa a gidan ibada na Tanzhesi daga wata duniya, wanda yake kunshe da tagulla da karfe masu wuyar samuwa. In an buga sassa daban daban a jikin kifin dutsen, to, ana iya sauraren kara daban daban masu dadin ji, sai kai ce kide-kide. Saboda haka ne bayan shekara da shekaru, wannan kifin dutse ya zama kifi mai tsarki a zukatan mutane, wanda ke iya abubuwa da yawa.


1 2 3