
Saboda haka, yawancin manazarta ba su nuna gamsuwa sosai kan sakamakon kwance damara da ake yi ba. Musamman ma, a watan jiya, a yayin da jirgin sama da ke daukar Mr. Soro a ciki ya sauka a filin jirgin sama a Bouake, an kai masa harin roka. Hakan ya nuna cewa, yana kasance da wasu 'yan hamayya da ba su goyi bayan yin sulhuntawa da gwamnatin ba. Har yanzu Cote d'Ivoire tana fuskantar boyayyun matsaloli wajen shimfida zaman lafiya.
Aiki mafi muhimmanci da ke gaban gwamnatin Cote d'Ivoire a yanzu shi ne yin babban zaben shugaban kasar cikin sauri. A farkon watan Yuli, Mr. Gbagbo ya ce, gwamantin ta iya yin babban zabe na gama gari ta hanyar dimokuradiyya a fili kuma cikin adalci kafin watanni 3 na farko na shekara mai zuwa. A gun bikin da aka yi a ran 30 ga wata, wannan shugaba ya nanata cewa, ya kamata jama'ar Cote d'Ivoire su share fage ga babban zaben da za a yi ta hanyar dimokuradiyya a fili kuma cikin adalci tun da wuri. Amma, masu nazarin al'amuran yau da kullum sun yi hasashen cewa, bisa fasahohin da aka samu daga kasashen Afirka da yawa a da, ma iya cewa, fadakar da jama'a kan harkokin siyasa a cikin zabe ya kan haifar da rikicin siyasa da kuma kawo baraka ga al'umma, musammam ma a kasashen da ke fama da rikicin al'umma mai tsanani, har ma ana gwagwarmaya da juna da makamai. Don haka, yadda za a tabbatar da masu kada kuri'a, da ko za a yi babban zabe ne cikin 'yancin kai da adalci kamar yadda ya kamata ko a'a, da kuma ko masu shan kaye za su amince da sakamakon zabe ko a'a da sauran batutuwa a jere za su jarraba 'yan siyasa na Cote d'Ivoire ta fuskar hikima da jaruntaka.(Tasallah) 1 2 3
|