Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-31 14:50:38    
Cote d'Ivoire na fuskantar wayewar gari wajen shimfida zaman lafiya

cri

A sakamakon shawariwari masu wahala na tsawon kusan shekaru 5 da kuma namijin kokarin da bangarorin da abin ya shafa suke ta yi ba tare da kasala ba, a karshe dai, jama'ar kasar Cote d'Ivoire da ke shan wahalhalun yake-yake suna fuskantar wayewar gari wajen shimfida zaman lafiya a kasarsu. Ran 30 ga wata, a filin wasa na birnin Bouake da ke arewancin kasar, kuma shi ne inda dakarun 'yan hamayya suka taba taruwa a da, an yi bikin kaddamar da kwance damara mai lakabi 'hasken zaman lafiya', wanda shi ne alamar sake dinkuwar kudanci da arewacin Cote d'Ivoire gaba daya.

A gun bikin da aka yi a ran nan, shugaba Laurent Gbagbo da firayin minista Guillaume Soro sun jefa bindigogi 2 a cikin wuta. Matakin da suka dauka ya nuna cewa, an shiga matakan a-zo-a-gani na kwance damara. Mr. Gbagbo ya yi wa mutane fiye da dubu goma a filin wasan bayanin cewa, an sa aya ga yakin basasa a Cote d'Ivoire a hukunce, yanzu an shimfida zaman lafiya a wannan kasa. Mr. Soro ya ce, wadannan makamai, iri ne na haddasa bala'i, kone su ya almantar da cewa, an kawo karshen yakin basasa. Ban da wannan kuma, shugabannin wasu kasashen Afirka da wasu jami'an harkokin diplomasiyya sun halarci bikin, inda suka ga zaman lafiya ya sauka a wannan kasa a idanunsu.


1 2 3