Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-31 14:50:38    
Cote d'Ivoire na fuskantar wayewar gari wajen shimfida zaman lafiya

cri
 

Wannan muhimmin biki ya kawo wa jama'ar Cote d'Ivoire da ke shan wahalar yake-yake kyakkyawan fata na zaman lafiya, haka kuma, ya shaida aniyar da gwamnatin Cote d'Ivoire da kungiyoyin 'yan hamayya suke nunawa a fannin neman samun zaman lafiya.

Ministan tsaro Michel Amani N'Guessan na kasar ya yi karin bayanin cewa, tun daga ran 30 ga watan Yuli zuwa ran 30 ga watan Agusta, za a yi wata daya ana gudanar da aikin kwance damara. Yanzu ko da yake dukkan rukunonin 'yan hamayya sun yarda da kwance damara, amma in an waiwayi duk ayyukan da ke shafar shimfida zaman lafiya a Cote d'Ivoire, ana iya ganin cewa, a kan gamu da matsaloli da yawa a lokacin da ake aiwatar da yarjejeniyoyi a da, shi ya sa mutane suka nuna damuwa kan ci gaban aikin kwance damara.

Tun bayan barkewar yakin basasa a Cote d'Ivoire a watan Satumba na shekarar 2002 har zuwa yanzu, ko da yake bangarori masu gwagwarmaya da juna sun sha daddale yarjejeniyoyin zaman lafiya daya bayan daya, don neman kawo karshen yakin basasa da kuma maido da zaman lafiya a wannan kasa, amma har yanzu ba a iya aiwatar da yarjejeniyoyin ba.


1 2 3