Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-30 15:38:31    
Sha'anin yawo shakatawa yana samun bunkasuwa a jihar Tibet bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet

cri

Wani labari daban shi ne yawan masu yawon shakatawa a jihar Tibet ya wuce miliyan 1.1 a cikin farkon rabin shekarar da muke ciki.

Hukumar yawon shakatawa ta jihar Tibet mai cin gashin kanta ta bayar da labari cewa, tun daga watan Janairu zuwa karshen watan Yuni, jimlar masu yawon shakatawa da suka kai ziyara a jihar ya kai fiye da miliyan 1 da dubu dari 1 a cikin farkon rabin shekarar da muke ciki, wato ya karu da kusan kashi 9 daga cikin kashi dari bisa na makamancin lokaci na shekarar da ta gabata.

Wani jami'in hukumar kula da harkokin yawon shakatawa ta jihar ya ce, bayan kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet a watan Yuli na shekarar 2006, an kawo karshen matsalar zirga-zirga da ta kasance a gaban sha'anin yawon shakatawa na jihar kwata kwata, wannan hanyar dogo ta taka muhimmiyar rawa wajen bunkasuwar sha'anin yawon shakatawa na jihar Tibet.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce, jimlar masu yawon shakatawa da suka kai ziyara a jihar Tibet a shekarar 2006 ya kai fiye da miliyan 2 da dubu dari 5, jimlar kudaden da jihar ta samu ya kuma kai kusan kudin Renminbi yuan biliyan 2.8.

A kwanan baya, jihar Tibet mai cin gashin kanta ta soma binciken abubuwan tarihi a tsanake a karo na 3.

Wakilin kamfanin dillancin labaru na Xinhua ya samu wannan labari ne a gun bikin kaddamar da binciken da aka yi a birnin Lhasa a ran 12 ga wata. Mukasudin yin wannan bincike shi ne ana sanin halin da abubuwan tarihi suke ciki a jihar Tibet, da kafa tare da kyautata adadin da yake da nasaba da abubuwan tarihi na kasar Sin da na jihar Tibet da abubuwan da suke cikin shiyoyyin kananan gwamnatocin jihar. Sannan za a iya kafa da kyautata matakan kiyaye abubuwan tarihi.

Wani jami'in hukumar harkokin abubuwan tarihi ta jihar Tibet ya bayyana cewa, za a yi wannan bincike ne har na tsawon shekaru 5. (Sanusi Chen)


1 2 3