An bayyana cewa, jihar Tibet tana da wuraren yawon shakatawa da gandun daji da albarkatun da ke cikinsu da yawa wadanda suke matsayin kasa. Yanzu gwamnatin jihar Tibet tana kokarin bude hanyoyin shan iska da ke kewaye da birnin Lhasa da shiyyar Linzhi da ta Rikaze da kuma tsohuwar hanyar da aka taba bi lokacin da kasar Sin take karkashin daular Tang, wato kimanin yau da shekaru dubu 1 da suka wuce da wata tsohuwar hanyar sufurin dokoki da ganyen shayi.
Wani jami'in hukumar yawon shakatawa ta jihar Tibet ya bayyana cewa, za a raya sha'anin yawon shakatawa a jihar Tibet ta hanyoyi iri daban-dabam. Sannan kuma lokacin da ake raya sha'anin yawon shakatawa a jihar, za a yi kokarin bayyana tarihi da al'adu da halin musamman na zaman al'ummar kabilu daban-daban da suke da zama a jihar Tibet.
1 2 3
|