A farkon watan Yuni da ya wuce, Malam Mike Rowse, shugaban hukumar kula da harkokin zuba jari ta Hong Kong ya bayyana a fili a gun wani taron manema labaru cewa, ya kamata, a kara ba da kwarin guiwa ga kamfanonin babban yankin kasar Sin da su bunkasa harkokinsu a Hong Kong. Ya ce, "muna ganin cewa, ya kamata, a kara bai wa kamfanonin babban yankin kasar kwarin guiwa don bunkasa harkokinsu a Hong Kong, ta haka za a hada kan bangarorin nan biyu a gu daya a fannin tattalin arziki. Yayin da muka ga babban kamfanin sayar da kayayyaki masu aiki da wutar lantarki na GOME yake bunkasa harkokinsa a Hong Kong, yana yin takara tare da kamfanonin Hong Kong, ta haka zai ba da taimako wajen kyautata kasuwannin sayar da kayayyaki da tsarin sana'o'I a Hong Kong. Wannan abu ne da muke fatan a samu."(Halilu) 1 2 3
|