Daidai kamar yadda Malam Zhou ya bayyana, kamfanonin Hong Kong sun kara samun bunkasuwa ta hanyar zuba jari a babban yankin kasar Sin. Alal misali, yawan 'yan kwadago da ke aiki a masana'antu da aka kafa bisa kudin jari na Hong Kong ya kai miliyan 15 a lardin Guangdong, wato ke nan ya ninka sama da sau biyu bisa jimlar mutanen Hong Kong. Malam Ye Jiequan, wakilin babbar kungiyar masana'antu ta Hong Kong ya ce, "taro kan aikin jawo kudin jari da babban yankin kasar ya shirya a Hong Kong ya kara samar wa masu aikin masana'antu na Hong Kong damar samun bunkasuwa ta hanyar zuba jari."
Malam Tang Yinnian, shugaban hukumar kudi ta Hong Kong ya bayyana cewa, Hong Kong yana da kyakkyawan tsarin kiyaye ikon mallakar ilmi da na samun kudaden jari, kuma yana ma'amala da kasashe masu yawa da sauransu. Daidai ne, kamfanonin babban yankin kasar da yawa suna sha'awar irin wadannan abubuwa masu rinjaye, sun dauki Hong Kong kamar wata hanyar da suke bi wajen shiga kasuwannin kasa da kasa.
1 2 3
|