Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-27 16:46:19    
Ana ta inganta hadin kai tsakanin Hong Kong da babban yankin kasar Sin a fannin tattalin arziki da cinikayya

cri

Hong Kong na kasar Sin shahararriyar cibiyar kudi da cinikayya da zirga-zirga ce a duniya, yana kan matsayi mai rinjaye wajen yin takara a fannin sadarwa da fasaha da kudin jari da sauransu, shi da babban yankin kasar Sin suna taimakon juna sosai wajen bunkasa harkokin tattalin arziki, kuma sun aza harsashi mai kyau ga hadin kansu. Bayan da aka komo da Hong Kong a karkashin mulkin kasar Sin a cikin shekaru 10 da suka wce, an yi ta inganta hadin kai a tsakanin Hong Kong da babban yankin kasar Sin a fannin tattalin arziki da cinikayya.

A kwanakin baya ba da dadewa ba, wakilai da suka fito daga lardunan Guizhou da Jiangxi da Hubei na kasar Sin sun shirya taro kan aikin jawo kudin jari a Hong Kong, inda suka gabatar wa kamfanonin Hong Kong da ayyuka daban daban da za a yi cikin hadin guiwa. Malam Zhou Wuchang, babban direktan hukumar jawo kudin jari ta birnin Anshun na lardin Guizhou ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na farko da muka shiga irin wannan taro a Hong Kong, mun sami sakamako mai kyau sosai. An cim ma yarjejeniyoyin hadin guiwa 18 a tsakanin birninmu da Hong Kong, wadanda suka shafi harkokin yawon shakatawa da zirga-zirga da ma'adinai da sauransu. Ya kara da cewa, "wannan ne karo na farko da muka zo Hong Kong, kuma mun sami sakamako mai kyau sosai, don haka nan gaba za mu sake zuwa. Wurinmu wuri ne mai arzikin albarkatun kasa kamar kwal da sauransu, kuma wutar lantarki da ake samarwa a wurinmu tana da rahusa sosai, sa'an nan kuma Hong Kong yana kan matsayi mai rinjaye a fannin sadarwa da kudin jari da fasaha, sabo da haka Hong Kong da babban yankin kasar suna iya taimakon juna a fannin tattalin arziki da cinikayya."


1 2 3