Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-26 19:24:22    
Farashin kayayyakin kasar Sin zai cigaba da hauhawa sannu a hankali

cri

Ya jaddada cewa, muhimmin dalilin da ya sa hauhawar farashin kayayyakin masarufi a cikin farkon rabin shekarar da muke ciki shi ne farashin abinci yana ta samun karuwa fiye da kima.

Bugu da kari kuma, Mr. Zhu Hongren, mataimakin direktan kula da harkokin cigaban tattalin arzikin kasar Sin a kwamitin neman bunkasuwa da yin gyare-gyare na kasar Sin ya ce, ko da yake tattalin arzikin kasar Sin yana cikin hali mai kyau daga duk fannoni, amma wasu matsaloli masu tsanani suna kasancewa har yanzu a fannin tattalin arziki. Alal misali, masana'antun narkar da karfe da ingantaccen karfe da na guba suna samun karuwa fiye da kima. Yawan kudaden da aka zuba domin samun kadarori ma yana ta karuwa fiye da kima. A waje daya, har yanzu ana amfani da fasahohin koma baya a wasu sana'o'i. Game da irin wadannan matsaloli, Mr. Zhu ya bayyana cewa, muhimmin aikin da gwamnatin kasar Sin za ta yi shi ne yin rigakafin bunkasuwar tattalin arziki fiye da kima a cikin sauran lokacin shekarar da muke ciki. "Dole ne mu mayar da aikin yin rigakafin bunkasa tattalin arziki cikin sauri fiye da kima zuwa aikin rigakafin bunkasuwar tattalin arziki fiye da kima lokacin da muke sa ido kan tattalin arziki daga duk fannoni. Kuma za mu ci gaba da kyautata da aiwatar da manufofin daidaita shi daga duk fannoni. A waje daya, za mu ci gaba da yin amfani da hanyoyin tattalin arziki da shari'a domin ba da jagoranci ga ci gaban tattalin arzikin kasar Sin." (Sanusi Chen)


1 2 3