Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-26 19:24:22    
Farashin kayayyakin kasar Sin zai cigaba da hauhawa sannu a hankali

cri

A makon jiya, bankin tsakiya na kasar Sin ya daga kimanin adana kudi da kimanin neman rancen kudi domin rigakafin karuwar saurin cigaban tattalin arziki fiye da kima bayan da aka bayar da saurin cigaban tattalin arzikin kasar Sin da aka samu a cikin farkon rabin shekarar da muke ciki.

Lokacin da ake tambayar ko tattalin arzikin kasar Sin zai samu cigaba cikin sauri fiye da kima, a gun wannan taron manema labaru, jami'an kwamitin neman bunkasuwa da yin gyare-gyare ta kasar Sin sun jaddada matsayin da gwamnatin kasar Sin ke dauka a kan wannan batu, wato saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin bai wuce kima ba. Mr. Shi Gang, direktan kula da tattalin arziki daga duk fannoni a kwamitin neman bunkasuwa da yin gyare-gyare na kasar Sin ya bayyana cewa, sakamakon da aka samu bayan da aka yi nazari ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana cikin hali mai kyau. Mr. Shi ya ce, "A ganinmu, yanzu tattalin arzikin kasar Sin yana cikin hali mai kyau. Alal misali, yawan kudaden da aka zuba a cikin farkon rabin shekarar da ta gabata domin samun kadarori ya karu da kashi 29.8 cikin kashi dari, amma a cikin farkon rabin shekarar da muke ciki, wannan adadi ya ragu ya kai kashi 25.9 cikin kashi dari. Haka kuma, tsarin tattalin arzikinmu ma ya samu sauye-sauyen da ake neman cimmawa. Bugu da kari kuma, jimlar kudaden cinikin kayayyakin masarufi ya karu da kashi 15.4 cikin kashi dari a cikin wannan rabin shekarar da muke ciki. Wannan karuwa ne mafi sauri da aka samu a cikin 'yan shekarun da suka wuce."


1 2 3