Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-26 19:24:22    
Farashin kayayyakin kasar Sin zai cigaba da hauhawa sannu a hankali

cri

Bayan hauhawar farashin abinci a kasar Sin, yanzu farashin kayayyaki da yawa yana ta hauhawa a cikin shekarar da muke ciki. Wannan ya sa tattalin arzikin kasar Sin ya kara fuskanta matsin lamba daga raguwar darajar kudi. A gun wani taron manema labaru da aka yi a birnin Beijing a ran 25 ga wata, jami'an kwamitin neman bunkasuwa da yin gyare-gyare na kasar Sin sun yi hasashen cewa, farashin kayayyaki zai ci gaba da hauhawa sannu a hankali a cikin sauran lokaci mai zuwa na shekarar da muke ciki.

A gun wannan taro, Mr. Cao Changqing, direktan hukumar kula da farashin kayayyaki ta kwamitin neman bunkasuwa da yin gyare-gyare na kasar Sin ya bayyana cewa, "Bisa halin da za a fuskanta a rabin shekarar da muke ciki ta biyu, muna ganin cewa, dalilan hauhawar farashin kayayyaki da dalilan raguwar kayayyaki suna kasancewa tare. Idan an kwatanta su, mai yiyuwa ne dalilan hauhawar farashin kayayyaki ya fi yawa. Amma, muna tsammani, farahin kayayyaki zai samu hauhawa sannu a hankali. Abin da ya fi muhimmanci wajen tabbatar da sakamakon karshe shi ne hatsi nawa da za mu iya samu a lokacin kaka."


1 2 3