Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-26 16:22:53    
Kong Zi da darikar Confucius(A)

cri

Me ya sa aka dauki Confucius a matsayin jagoranci a kullum a zamanin gargajiya na kasar Sin.Da wuya a bayyana shi kwata kwata.A takaice dai tuaninsa na nuna wariya tsakanin mutane da kawo sauyi ga harkokin siyasa ya biya bukatun masu tafiyar da mulkin gidajen sarauta,ya kuma taimakawa zaman kwanciyar hankali na jama'a da daukaka cigaban zamantakewa.Bisa darikar Confucius,dole ne mabiya su bi shugabanni,da ya bi ubansa,in ba haka ba su aikata laifi.Bisa darikarsa ya kamata sarki ya tafiyar da harkokin mulki yadda ya kamata,farar hula su yi biyayya ga sarki.Ya ce kowane mutum yana da nasa matsayi da dama,ya iya zama da,ko uba ko waziri.in yana cikin wani matsayi,sai ya yi abin da ya kamata ya yi.Ta haka za a iya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa.

Da darikar Confucius ta fito ba a dauke ta a matsayin tunanin jagoranci nan da nan a wancan zamani ba.Sai a karni na biyu kafin bayyanuwar Innabi Isa da aka sami wata hadaddiyar daula dake da gwamnatin tsakiya ke mulki.Masu mulki sun gano darikar Confucius na da amfani kwarai wajen kiyaye oda da kwanciyar hankali na jama'a,sai sun dauke shi a matsayin tunanin jagoranci a kasar da suke mulki.(Ali)


1 2 3