Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-26 16:22:53    
Kong Zi da darikar Confucius(A)

cri

Kong Zi wani mutumin ne da ya kafa darikar Confucius a kasar Sin kafin shekaru dubu biyu da suka gabata.Har wa yau dai ba ma kawai a harkokin iyasa da na al'adu ake iya samo tasirinsa har ma ana iya ganins tasirin wannan darika a dabi'un Sinnawa da tunaninsu.Shi ya sa wasu masanan kasashen ketare sun dauki tunanin Confucius tamkar darikar addini na kasar Sin.A hakika Confucius ba addini ba ne wani falfasa ne wanda yana daya daga cikin dariku da dama na gargajiya na kasar Sin.Duk da haka a cikin shekaru fiye da dubu biyu da suka shude,gidajen sarauta na kasar Sin sun dauki darikar Confucius kamar tunanin jagora kuma aka nuna masa girmamawa cikin dogon lokaci.

Confucius ba ma kawai ya haifar da babban tasiri ga al'adun kasar Sin ba har ma ga wasu kasashe na Asiya.Duk inda Sinnawa ke zaune a gida da waje, ana bin darikar Confucius a kullum.Duk lokacin da ake tabo batun al'adun Sin na gargajiya,tabbas ne sai an ambatci sunan Kong Zi wanda ya kafa darikar Confucius.A shekaru 70 na karnin da ya shige yayin da wani masanin Amurka ya tsara jerin jadawalin manyan mutane na tarihi na Bil Adam,ya sa sunan Confucius a cikin wanda yake matsayi na biyar bayan Jesus Christ da ya kafa addinin Katolika da Sakyamuni da ya kafa addinin Buddha.Ga mutanen Sin,Confucius yana gaba domin yana adabar kowa da kowa.


1 2 3