An haifi Kong Zi wanda ya kafa darikar Confucius ne a shekara ta 551 bayan bayyanuwar Innabi Isa,ya rasu a shekara ta 497,bayan shekaru sama da dari an haifi wani mashahurih Falfasa na kasar Greek Aristode.Uban Kong Zi ya rasu yayin da ya kai shekaru uku da haihuwa,daga bisani uwarsa ta dauki shi zuwa wani wuri na lardin Shandong na kasar Sin na zamanin yau.Kong Zi yana da wani sunan daban wato Kong Qiu.Ana kiransa Kong Zi ne domin daukaka sunansa da nuna girmamawa gare shi.
A zamanin Kongzi da akwai kanana kasashe da dama a kasar Sin ta yanzu,Kong Zi ya yi zama a kasar Lu wadda ta fi cigaban al'adu a wancan zamani.
Da ya ke Kong Zi yana da ilimi mai zurfi a wancan zamani,amma bai sami wani mukami ba a duk rayuwarsa.A zamanin da, a kasar Sin dattijai kawai ne ke da ikon samun ilimi.Kong Zi ya karya wannan ikon musamman da hanyarsa.Ya tattara almajirai ya yi musu lacca,duk wani almajiri ko shi mai arziki ne ko kowa shi matalauci in ya ba da kankanin wani abu kamar kudin karatu ya iya samun karatu a wurinsa.Kong Zi ya fadakar da kan almajiransa da tunaninsa na siyasa da darika.An ce ya samu almajirai dubu uku,daga cikinsu wasu sun zama manyan masana kamar yadda Confucius wadanda suka gaji tunaninsa da bunkasa shi da kuma yawaita shi a ko ina.
1 2 3
|