Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-25 08:28:46    
Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin tana yin aikin share fage domin shiga gasar cin kofin duniya

cri

Kamar yadda kuka sani,gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata ita ce gasa mafi matsayin koli a duniya,kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta taba samun zama ta biyu a gun gasar a shekarar 1999.Daga baya kuma ta koma baya a kai a kai.Yanzu dai za a yi gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata ta shekarar 2007 a kasar Sin,ko shakka babu kungiyar kasar Sin za ta yi iyakacin kokari domin shiga kungiyoyi hudu mafiya karfi.Kodayake kungiyar kasar Sin ta riga ta sami ci gaba,amma ya kasance da wasu matsaloli,alal misali,jikin `yan wasan kasar Sin ba su da karfi sosai,ban da wannan kuma,karfinsu na yin takara a cikin muhimmiyar shiyya ba shi da kyau.Domanski ta bayyana cewa,a cikin watanni biyu masu zuwa,za su mai da hankali kan wadannan matsaloli.Ta ce:  `A cikin watanni biyu masu zuwa,za mu yi kokarin kyautata ingancin jikin `yan wasanmu,ban da wannan kuma,za mu kyuatata fasahar wasanmu wato mu yi jigilar kwallo cikin sauri,a karshe dai,za mu kara karfin shigar da kwallo cikin raga.`

Yanzu,kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin tana yin gasanni a jere domin gwajin sakamakon horarsu,ko za ta ci nasara a gun gasar cin kofin duniya?Bari mu sa ido mu gani.(Jamila Zhou)


1 2 3