Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-25 08:28:46    
Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin tana yin aikin share fage domin shiga gasar cin kofin duniya

cri

A watan Satumba na shekarar 2007 wato shekarar da muke ciki,za a yi zama na 5 na gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata a kasar Sin.Wannan ita ce gasa mafi girma da kasar Sin ta shirya kafin taron wasannin Olimpic na shekarar 2008 da za a yi a birnin Beijing,babban birnin kasar Sin.Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin tana sanya matukar kokari domin wannan.Kwanakin baya ba da dadewa ba,a gun gasar kwallon kafa ta mata dake tsakanin kasashe hudu da aka shirya bisa gayyata,kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta sami cikakkiyar nasara kuma ta zama zakara,wato ta nuna wa kasashen duniya karfinta.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.

Kwanakin baya ba da dadewa ba,an shirya gasar wasan kwallon kafa ta mata tsakanin kasashe hudu bisa gayyata a birnin Qinghuangdao da birnin Shenyang dake arewacin kasar Sin,an kiran gasar da sunan `Beijing mai sa`a`.Wadanda suka halarci gasar suka hada da kungiyar kasar Sin da ta kasar Mexico da ta kasar Italiya da ta kasar Thailand.A gun gasar,kungiyar kasar Sin tana cikin hali mai kyau,a zagaye na karshe na gasar,ta lashe kunigyar kasar Mexico da 1 bisa 0 ta zama zakara.Bayan gasar,mai jagorancin kungiyar kasar Mexico Gonzalez Canales ta bayyana cewa,  `Kungiyar kasar Sin tana da karfi,ana iya cewa kungiyar kasar Sin tana sanya matukar kokari a ko da yaushe,ko shakka babu za ta sami ci gaba.Ban da wannan kuma,mun tarar da cewa `yan wasan kasar Sin suna iya shigar da kwallo da kai sosai,duk da haka,kungiyar kasar Sin ita ce kungiya mai hadari wajen yin takara.`


1 2 3