Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-25 08:28:46    
Kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin tana yin aikin share fage domin shiga gasar cin kofin duniya

cri

Dalilin da ya sa kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta sami ci gaba da saurin haka shi ne domin kokarin da babbar malamar wasa Marika Domanski ta yi.

Babbar malamar wasa Domanski ta zo ne daga kasar Sweden,tun daga watan Aflilu na shekarar bana,ta fara aikinta na babbar malamar wasa ta kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin.Nufinta shi ne kungiyar kasar Sin za ta sami sakamako mai kyau a gun gasar cin kofin duniya da za a yi a watan Satumba na bana.A cikin watanni uku da suka gabata,kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta riga ta sami ci gaba a bayyane,Domanski ita ma ta gamsu da aikinta.Ta ce:  `A halin da ake ciki yanzu,muna yin aikin share fage domin shiga gasar cin kofin duniya,abu mai faranta ran mutane shi ne mun riga mun sami ci gaba wajen sauri,wato yanzu `yan wasanmu suna iya yin wasa da karfi kuma cikin sauri.Ina jin dadi.`

Ban da wannan kuma,a kullum,Domanski tana mayar da wasan kwallon kafa a matsayin wasa mai sanya ta farin ciki,sau tarin yawa ne ta sa kaimi ga `yan wasan kungiyarta da cewa,kamata ya yi su ji dadin wasan kuma su ji dadin gasa.A karkashin kokarinta,`yan wasan kungiyarta suna kara jin dadi kuma dangantakar dake tsakaninsu tana kara kyautatuwa.

Bayan da kungiyar wasan kwallon kafa ta mata ta kasar Sin ta zama zakarar gasar da aka shirya bisa gayyata,`yan wasa suna kara cike da imani.


1 2 3