Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-24 15:41:26    
Fahimtar halayen gargajiya na kananan kabilu a jihar Inner Mongolia

cri

An dauki sa'o'i 3 ko fiye zuwa fili mai ciyayi na Gongbaolage na Xilinguole a jihar Inner Mongolia daga nan Beijing cikin mota, wanda fili mai ciyayi ne na halitta mafi kusa da Beijing. A shekarun baya da suka wuce, makiyaya suna raya aikin yawon shakatawa sannu sannu a fili mai ciyayi da suke zama a kai, masu yawon shakatawa na iya rayuwa a gidajen makiyayan.

'Yan kabilar Mongolia suna karbi baki da hannu biyu biyu. In sun yi bakunci, mai gida ya kan yanka tumaki, ya dafa namunsu, ya samar da giyar da ya yi da madara da kuma abincin madara da 'yan kabilar Mongolia makiyaya suka saba ci. Gasasshen naman tumaki abinci ne mai kyau domin samar wa baki.

Ban da kyan karkara a filaye masu ciyayi a jihar Inner Mongolia, in kuna son kara fahimta kan al'adun gargajiyar kabilar Mongolia, to, bikin Nadamu da a kan shirya a wurare daban daban a jihar Inner Mongolia a ko wace shekara ya fi nuna sigar musamman ta al'adun gargajiyar wannan kabila. A bakin 'yan kabilar Mongolia, ma'anar Nadamu ita ce nishadi. A ko wane lokacin zafi, makiyaya sun taru a filaye masu ciyayi domin tseren dawaki da kokawa da yin gasar harbar takobi, dukkan wadannan harkoki suna da nasaba da al'adun gargajiya na kabilar Mongolia mai tsawon shekara da shekaru.

A lokacin zafi na wannan shekara, an yi kasaitaccen biki domin murnar cikon shekaru 60 da kafuwar jihar Inner Mongolia mai cin gashin kanta a filaye masu ciyayi. A lokacin can, za a kira harkoki fiye da 70 a wurare daban daban a wajen. Malam Yun Daping ya yi bayani game da wadannan harkoki, ya ce,

'Za mu shirya bikin kasa da kasa kan al'adu irin na fili mai ciyayi a karo na 4, da gasar rera wakokin makiyaya ta kasar Sin a karo na farko. Haka zalika kuma, za a yi bikin Nadamu a karo na 18 ta jiharmu tun daga ran 25 zuwa ran 31 ga watan Yuli da bikin fasahar tufafi da kayayyakin ado na kabilar Mongolia na kasar Sin da bikin ruwa mai tsarki na babban dutsen Aershan da kuma bukukuwan nune-nunen nagartattun kayayyakin gargajiya na babban tsaunin Hongshan a jere.'(Tasallah)


1 2 3