Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-24 15:41:26    
Fahimtar halayen gargajiya na kananan kabilu a jihar Inner Mongolia

cri

A zuciyar Wang Yi, abubuwan da ke fi burge shi a filaye masu ciyayi na Inner Mongolia su ne kyan ganin filayen masu ciyayi da kuma kishin karbar bakunci da 'yan kabilar Mongolia ke nunawa. A filayen ciyayi masu fadi, wadanda ba a iya ganin iyakarsu ba, makiyayya sun fi son karbar bakunci. Da zarar shigar mutane cikin gidan wani makiyayi, sai uwar gida ta soma dafa naman tunkiya da kuma shayi tare da madara ta hanyar da 'yan kabilar Mongolia suka saba bi a fannin karbar baki. A lokacin cin abinci, wajibi ne mai gida ya rera waka domin bai wa baki giya bisa matsayin koli ta fuskar karbar baki, tare da wani kwanon azurfa a hannunsa, wanda cike yake da giyar da suka yi daga madara da kansu.

Babu tantanma fahimtar halayen gargajiya na kabilar Mongolia a filaye masu ciyayi a Inner Mongolia ya yi kyau kwarai ga 'yan birni. Mataimakin shugaban hukumar harkokin yawon shakatawa ta jihar Inner Mongolia malam Yun Daping ya yi karin bayanin cewa,

'Mutane su kan dauki mintoci misalin 45 daga Beijing zuwa birnin Huhehaote cikin jirgin sama, ta hanyar mota kuwa su kan bukaci sa'o'i misalin hudu da rabi, haka kuma, tsawon lokacin da su kan kashe cikin jirgin kasa ba ya kai sa'o'i 11. Ba za su gamu da matsaloli ba wajen zuwa filaye masu ciyayi, inda za su more idannu da kyan karkara. Mun shimfida hanyoyin mota a ko ina a jiharmu, za su sami sauki.'


1 2 3