Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-24 15:41:26    
Fahimtar halayen gargajiya na kananan kabilu a jihar Inner Mongolia

cri

A jihar Inner Mongolia mai cin gashin kanta da ke karkara a arewacin kasar Sin, akwai hamada mai fadi da kyawawan tabkuna da kuma kayayyaki gargajiya da wuraren gargajiya masu yawa. A cikin shirinmu na yau, bari mu je wannan jiha domin kara fahimtar halayen gargajiya na kananan kabilun Sin.

'Yan kabilu 49 da suka hada da kabilun Mongolia da Han da Hui da Man da dai sauran kananan kabilu 45 suna zaune a jihar Inner Mongolia, a ciki yawan 'yan kabilar Mongolia ya wuce miliyan 4. Idan masu yawon shakatawa suna son fahimtar halayen gargajiya na kabilar Mongolia a wajen, to, tabbas ne su je filaye masu ciyayi. Manyan filaye masu ciyayi da Xilinguole da Hulunbeier da Keerqin sun dade sun shahara a gida da kuma a ketare. Malam Wang Yi, wanda ya zo daga birnin Beijing, ya bayyana ra'ayinsa kan filaye masu ciyayi a jihar Inner Mongolia, ya ce,

'Na ji matukar farin ciki a lokacin da nake ziyara a fili mai ciyayi a Inner Mongolia. Kyakkyawan muhalli da makiyayya masu kirki da kuma zaman rayuwarsu sun burge ni sosai.'


1 2 3