Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-07-20 15:37:50    
Birnin Zhongqing ya sami babban ci gaba tun bayan da aka mayar da shi a karkarshin shugabancin gwamnatin kasar Sin kai tsaye

cri

Bari mu yi misali da unguwar Dadukou ta birnin, yau da shekaru 10 da suka wuce, fadin unguwar ya kai muraba'in kilomita 7 kawai, tana da hanyar mota daya tak, ba ta da wasu gine-ginen za a zo a gani. Yanzu fa, unguwar ta riga ta sami manyan sauye-sauye, har ta zama wata unguwa ta zamani. Ga tagwayen hanyoyin mota da hanyoyin jiragen kasa masu zirga-zirga cikin gari da manyan gadoji da kuma manyan gine-gine masu kyau a ko ina cikin unguwar. Fadinta ma ya habaka ya kai muraba'in kilomita 103. Unguwar Dadukou ta gwada irin ci gaba da birnin Zhongqing ta samu. Malam Zhou Yuan na birnin ya nuna babban yabo cewa, "bayan da aka mayar da birninmu a karkashin shugabancin gwamnatin kasar Sin kai tsaye ashekarar 1997, gwamnatin ta kashe makudan kudade wajen yin manyan ayyuka wadanda suka hada da hanyar jirgin kasa mai zirga-zirga a birnin. A da birninmu ya gina gadoji biyu a kan koguna kawai, daya yana kan Kogin Jialinjiang, saura daya kuma a kan Kogin Yangtse. Yanzu, birnin ya sake gina gadoji da yawa, ta haka muna yin zirga-zirga cikin sauki. Alal misali, a da, in an tashi daga wuri mai suna Jiefang zuwa unguwar Dadukou cikin bos, sai an yi awa daya da wani abu, amma yanzu tafiyar mintoci 10 da wani abu kawai."

A watan Maris da ya wuce, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya taba gabatar da cewa, "ya kamata, a gaggauta raya birnin Zhongqing da ya kasance muhimmin sansani da ke kara samun bunkasuwa a yankunan yammacin kasar Sin, da cibiyar tattalin arziki a yankunan mafarin Kogin Yangtse, don cim ma manufar samun wadatuwa daga duk fannoni a yankunan yammacin kasar Sin tun da wuri.(Halilu)


1 2 3