![]( /mmsource/images/2007/07/20/birni3.jpg)
A watan Maris na shekarar 1997, an mayar da birnin Zhongqing da ya zama birni da ke karkashin shugabancin gwamnatin kasar Sin kai tsaye. An yi haka ne domin biyan bukatu da ake yi wajen gudanar da ayyukan tsare ruwa na Kogin Yantse a Sanxia, da daidaita batutuwan sake tsugunar da mazauna miliyan da ke zama a wurare da aka gina matarin ruwa na Sanxia, da kuma kiyaye yanayin kasa da sauransu. Birnin Zhongqing wani babban birni ne mai yawan mutane sama da miliyan 30, fadinsa kuma ya wuce muraba'in kilomita 80,000. Gwamnatin kasar Sin ta zuba makudan kudade don ba da taimako wajen raya shi.
Da Malam Yang Qingyu, shugaban hukumar kula da harkokin bunkasuwa da gyare-gyare ta birnin Zhongqing ya bayana ra'ayinsa a kan ci gaba da birnin ya samu wajen bunkasa harkokin tattalin arziki a cikin shekaru 10 da aka mayar da shi da ya zama birni da ke karkashin shugabancin gwamnatin kasar Sin kai tsaye. Ya ce, "a cikin shekaru 10 da aka mayar da binrin Zhongqing ya zama birni da ke karkashin shugabancin gwamnatin kasar Sin kai tsaye, birnin ya sami bunkasuwa cikin sauri har ba a taba ganin irinta ba a da. Sa'an nan kuma shekarun nan 10 shekaru ne da mazaunan birnin suka amfana kwarai."
1 2 3
|